Tun daga sanya sutura mace za ta iya fahimtar halayen saurayin da ya zo zance wajen ta.. cewar marubuciya Princess supheeah

Assalamu alaikum Barka da zuwa shafin littafanyaki.com.ng

Muna yiwa bakuwarmu Barka da zuwa da farko za mu so mu ji takaitaccen tarihin bakuwarmu?


Wa'alaikumus Salam 

Ina ma kowa fatan alkhairi ya ibada kuma

Da farko dai Suna na Safiyya Muhammad wadda aka fi sani da Princess Supheeah 

An haifeni a Karamar hukumar Kurfi Katsina State nayi Primary school dina anan cikin garin kurfi Secondary school Kuma nayi makarantar kwana wadda ke cikin garin Dutsinma na gama Secondary Dina 2018 sannan na tafi College shima 2021 nayi graduate ln da na karanta Islamic English 

Kusan shekara daya kenan da gamawa amma yanzun kuma lna yan sana'o'in irin namu na mata dan zaman ba sana'a ba dadi.


Zuwa yanzu kin wallafa littafai nawa kuma mene ne adadin su wanne ne bakandamiyar ki ?

Zuwa yanzun na yi littattafai a ƙalla guda huɗu

1- Saki kowa kama Allah

2- Matar Mahaifi Na

3- Wata Rayuwa

4-Ameesha


Bakan damiya ta shine Saki kowa Kama Allah sannan matar mahaifi na

A matsayin ki na ya mace Ko bakuwar mu ta taɓa haduwa da wani kalubale ga maza makarantan ki ?


Gaskiya ban taba fuskantar kalubale ba a fannin makaranta ta saboda duk wanda muke karatu dasu irin manyan mutane ne kuma suna mutunta matan cikin su dan kowa ma harkan gaban sa yake ldan ba ko irin ana so a kara ma juna sani ba a harkan.

A bangaren nau'in abincin gargajiya shin wanne bakuwar mu take so ?


Hhhh Abincin gargajiyar da nake so 

Wasa-wasa da wake da mai da yaji 😋

Da wane salo kike rubutu kuma wane nasarori kika samu


Ina amfani da salon Zaman takewa na rayuwar da muke ciki musamman irin mutanen mu mazauna ƙauye da kuma irin rayuwar ko ln kula da ake yi da neman ilimin Mata na addini da na zamani.

Wane rubutu kika taɓa yi da kike alfahari da shi ?


Rubutun da nayi kuma nake alfahari da shi gaskiya shine Rubutun da nayi na matar Mahaifi na. Gaskiya lna alfahari da wannan.

Shin kin taba fuskantar kalubale ga gida ko wani dangi game da zamowar ki marubuciya?

Gaskiya ban fuskanci ƙalubale ba daga gida ko a cikin dangi, dan ma suke bani kwarin gwiwa yin rubutun da sunga na kwana biyu banyi ba zasu fara tambaya na meyasa meye dalili a haka suke bani kwarin gwiwa.

A matsayin ki na mace shin me kike gani ya haddasa rashin haɗin kan marubuta ?

A matsayi na na marubuciya mace,

Abun da yake haddasa rashin hadin kai abu daya zuwa biyu

Manyan marutan mu suna da girman kai ko nace suna nuna ko ln kula ga ƙananan marubutan su

Idan za ki bawa wacce zata fara rubutu shawara da me ya kamata ace ta fara?


Zan fara bata shawara ta fara da Bakaken Hausa sannan ƙa'idojin rubutu.

Shin wane ne ganin ki a marubuta maza?


Abdul'aziz Sani Madakin gini.

Kun taba yin rubutun yaki ko kuwa kina sha'awar yin sa?


A'a gaskiya ban taɓa yi ba amma lna Sha'awar yin.

A tunanin ki mene ne ke kawo rashin haɗin kai tsakanin marubuta?


Rashin hadin kai marubuta girman kai shine kesa rashin hadin kan marubuta.

Ko bakuwarmu na da aure ? Ko ana niyyar yi?

Ni allurar cikin ruwa ce Mai rabo ka dauka 😀

To a matsayin ki na budurwar

Ko za ki iya mana bayani akan wane ne hali yan mata ke shiga idan suka shiga jinkirin aure 

Samun mane mi?


Halin da ƴan mata ke shiga na jinkirin Aure wasu na shiga ma wuyacin hali musamman waɗanda iyayen su suke matsa masu su fito da mijin Aure ko suna ganin sun tsaya ruwan ido ne irin su sunfi shiga mawuyacin hali 

Sai kuma irin masu zama gida a ko da yaushe gida ana ta ƙura masu basa zuwa ko lna daga gida sai gida anan ne mutum zai ji ldan yayi aure hakan bazata faru ba ko baza ana takura maka ba akwai kuma iyayen da sun gaji da ƴaƴan ne sungaji da zaman su a gidan suma yaran sai kaga suna shiga damuwa sunajin koma wa yazo zasu iya auren sa su huta da matsin da ake masu a gida.

Wace shawara za ki yanmatan da kuma iyaye?

Shawarar da zan ba ƴan mata shine kawai su dage da addu'a Allah yana jin su kuma yana ganin su wani jinkirin alkhairi ne 


Sannan suci gaba da hakuri da duk halin da suka tsinci kansu sannan su rike mutuncin su da tarbiyyar da iyayen su sukayi masu 

Su kuma iyaye su ci gaba da yi mana addu'a da kuma hakuri da mu

Ba abun da ya taɓa dawwama a rayuwa wata rana sai labari.

A matsayin ki na matashiya shin me kike tsammanin ya haifar da rashin aure tsakanin matasa maza.

Rashin kudin auren ko kuma dogon buri ga maza ko mata ?

 Dogon buri da rashin aikin yi 

Su suka haifar da rashin aure ga maza Da mata kowa yana so yayi kudi lokaci daya kowa ji yake ina ma da ya bude ido ya ganshi da kuɗi kowa kuɗi mazan da matan 


Ita mace tana ganin baza ta iya auren wanda baya da kuɗi ba 


Su kuma mazan sai son suyi kudin amma basa tashi sune ma.

Ga yara ƙanana mata ya ya kamata iyaye mata su kula da su a lokacin fara al'ada ?

Sosai ma kuwa ya kamata su kula dasu su nunnuna masu abun da ya kamata suyi lokacin sunayi da wanda zasuyi idan al'adar.

Waɗanne halaye ya kamata kowacce budurwa ta gari ta lura da su a lokacin da saurayi ya zo neman auren ta ?


Abu na farko da mace zata lura da saurayi ldan ya fara zuwa wajen ta yanayin kayan da yasa da kasan a sa kaya ma anan ana fara gane shin kai wane kalan mutum ne da kuma yanayin kalaman dake futa daga bakin sa da kuma natsuwar sa su zata fara kalla duk da hali ba lokaci daya mutum zaka fahimci waye yake maka magana ba.

A tunanin ki mene ne ya sanya wasu mazan sabbin aure ba su san matan su samu juna biyu,

Shin wayewa, boko ko kuma jahilci.


Jahilci ne kesa mutum yace baya son Matar sa su samu juna biyu da wuri jahili ne bazaiyi tunanin ma yana haihuwa ko Bama yayi shin wannan tsarin haihuwar da zanyi yana ga illa da wacce bata tabayi ba ko baya dashi da yana da ilmi tunani zai yi kafin ya aikata.

Mene ne fatan ki a duniyar rubutu ?


Ina ma kowa fatan alkhairi Allah ya kuma ya cika ma kowa burin sa na alkhairi.

Saƙon ki ga makaranta da marubuta yan uwan ki ?


Sakona ga ƴan uwana marubuta shine su san me suke rubutawa wanda zai amfani al'umma


Muna godiya da ziyarar shafin mu da fatan za ki sha ruwa lafiya


Nima lna godiya sosai 


Amin ya hayyu ya qayyum birahmatika astagith Allah ya karba mana ibadun mu.

Post a Comment

0 Comments