Auren marubuci ba a kiba kuma ya danganta wa Allah ya zaɓa maka..


 Auren marubuci ba a ƙiba kuma ya danganta wa Allah ya zaɓa maka..

Zahra T Fresh 

Assalamu alaikum Barka da zuwa shafin littafanyaki.com.ng

Muna yiwa bakuwarmu Barka da zuwa da farko za mu so mu ji takaitaccen tarihin bakuwarmu?

Wa'alaikumussalam warahamatullah.

Barkan mu dai , ina matuƙar godiya da gayyata.

Da farko dai sunana Fatima Abdullahi Shadai

( Zahra T. Fresh)

Kuma ni ƴar garin Kano ce mazauniyar ƙaramar hukumar Dawaki Kudu.

Na yi karatuna tun daga matakin primary har zuwa na Secondary, a garin Dawakin Kudu, inda a halin yanzu nake matakin karatun (N.C.E) a makarantar N.T.I Kaduna.

A bangaren nau'in abincin gargajiya shin wanne bakuwar mu take so ?

To a ɓangaren abincin gargajiya na fison.

Ɗan wake, Dambu, kunu da ƙosai.

Zuwa yanzu kin wallafa littafai nawa kuma mene ne adadin su wanne ne bakandamiyar ki ?

Gaskiya dai yanzu na fara, na rubuta littafi guda ɗaya

 Matan Ramadan.

Shine nake wallafa wa yanzu, bakandamiya kuma zan iya ce wa Matan Ramadan duba da yadda yake samun karɓuwa sosai.

A matsayin ki na ya mace Ko bakuwar mu ta taɓa haduwa da wani kalubale ga maza makarantan ki ?

Ban taɓa samu ba gaskiya, ina zaune lafiya dasu.

Wane rubutu kika taba yi da kike alfahari da shi ?

Zan iya ce wa Matan Ramadan, ahalin yanzu bansan kuma nan gaba ba.

A matsayin ki na mace shin me kike gani ya haddasa rashin haɗin kan marubuta ?

Gaskiya zan iya ce wa girman kai da kuma san kai, sai rashin taimakon na ƙasa.

Wannan yana ɗaya dayake kawo rashin haɗin kan marubuta.


Duk da daima yanzu marubuta suna girmama junansu sosai, amma dai har yanzu da bara gurbi a ciki.

Bakuwarmu ko ta na da aure ko kuwa ana kan hanya 

Kina da ra'ayin ƙi auren dan uwan ki marubuci ?

To gaskiya ana dai kan hanyar.

To bazance ina da ra'ayin ƙin auren Marubuci ba, ya dai danganta da wanda Allah ya zaɓawa mutum.

Ko dai marubucin ko ba marubucin ba, na gari dai ake so.

Mene burin ki a rubutu?

Burkina bai wuce na rubuta abinda zai amfani al'ummar musulmi, wanda duk wanda ya karanta littafina zai amfana da wani abin arayuwa, idan kuma mutum yana aikatawa yazama ta sana diyyar littafina ya daina, ko kuma ya rage.

Sannan kuma littafina yaje inda ban taɓa zaton zai je ba, dan mutane su amfana.

Shin kina da ubangida a rubutu?

E, ina da ubangida a rubutu, wanda shi na fara sani, kuma shine salir kawo wata i yanzu.

*_ Jibrin Adamu Jibrin Rano_*

Sai kuma wanda yace zai fara koyamin rubuta littafin yaƙi.

*_Mansur Usman Sufi_*

_(Sarkin marubutan yaƙi)_


Mene ne muhimmancin sakon ki ga marubuta ga makaranta

Muhimmin saƙo na ga marubuta shi ne

Su dage kai da ƙafa wajan rubuta abinda zai amfani al'ummar musulmi, ya faɗakar.

Sai kuma masu rubutun batsa da su ji tsoron Ubangiji su daina, rubuta irin waɗannan littafin suma, su dawo kan hanyar faɗakarwa, don shi marubuci Malami ne.

Marubuta muna da haɗin kai da san juna to dai muƙara akan nada.

Sai kuma makaranta, suma su dage wajan karanta labarinda zai amfane su ba wanda zai cutar da su ba, irin littafin batsa.

_Allah ya ƙara mana basira , Allahumma Amin_


Post a Comment

0 Comments